Ahmad Hamisu Gwale
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya da jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun halarci Jana’izar Marigayi Ahmadu Haruna Zago, da aka gudanar a kofar Kudu fadar Sarkin Kano.
Cikin wadanda suka halarci Jana’izar har da Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na biyu, da mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo da shugaban majalisar dokoki Jibril Ismail Falgore da sauransu.
Kafin Rasuwarsa Ahmadu Haruna Zago da aka fi sani da Dan Zago, shi ne shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, kuma ya rasu ne bayan fama da jinyai a asibitin Mallam Aminu Kano da ke jihar.
Dan Zago an fi saninsa a fagen gwargwarmayar siyasa, wanda da ya riƙe muƙamai daban-daban a fagen siyasa.
A baya ya rike mukamai da dama, ciki har da rike shugaban tsohuwar jamiyyar ANPP na jihar Kano, sannan shi ne tsohon mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan hakokin siyasa.
Tuni dai ake ci gaba da mika sakon ta’aziyya ga iyalan Marigayi Ahmadu Haruna Zago, kuma gwaman Kano Abba Kabiru Yusuf shima ya mika nasa sakon ta’aziyyar.
