Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano ya ziyarci unguwar Kofar mata inda aka yi fama da fadace-fadacen ‘yan daba.
Fadan wanda aka ce ya samo asali daga wasan kwallon kafa da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke unguwar a ranar Lahadi
Fadan ya kuma cigaba tsakanin ‘yan daba daga unguwannin Yakasai da Zage da kuma Zango a inda suka bi a ta Kofar Mata suna sara da suka kan mai uwa-da-wabi.
Wanda hakan ya haifar da kisan wasu mutane uku a cewar wani rahoto.
Kwamishinan ya kai ziyara unguwar Kofar mata da kuma bayar da umarnin gudanar bincike kan lamarin da kuma wadanda ke da hannu inji.
Ziyarar ba zai rasa nasaba da zuwa ofishin nasa cikin gaggawa ba da Mai unguwar Kofar mata shi wasu ‘yan unguwar da suka kai masa ziyara kan lamarin tun da farko.