
Wasu kungiyoyin rajin kawo ƙarshen cin hanci da rashawa sun yi Allah wadai da hukucin babbar kotun jihar Kano da ke Bichi bisa jagorancin mai shari’a, Musa Ahmad, suna masu zargin cewa hukuncin ya bai wa wani babban jami’in gwamnatin Kano da ake zargi da almundahanar biliyoyin kuɗi kariya.
A ranar 18 ga watan Agusta, mai shari’ar ya dakatar da hukumar ICPC da EFCC daga binciken Abdullahi Rogo, daraktan tsare-tsaren ayyukan gwamnan Kano, Abba Yusuf.
Sai dai ICPC da EFCC sun musanta zargin da ya yi na yi masa barazana domin hukunta shi a maimakon bincikensa da suke son yi.
Sun ce kawai sun gayyaci Rogo ne domin ya zo ya yi bayani game da ko yana da hannu wajen karkatar da wadannan kuɗi.
Wannan shari’a ta sha suka daga kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa inda suka bayyana hukuncin da yi wa yaƙi da cin hanci a ƙafar ungulu.
Jaridar Premium times ta rawaito shugaban kungiyar ci gaban ɗan’Adam da muhalli ta HEDA, Olanrewaju Suraj, na cewa, hukuncin daidai yake da yin watsi da yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ya zargi masu riƙe da muƙamai da amfani da umarnin kotu wajen kaucewa wa bincike, inda ya buga misali da ta tsohuwar ministar sufurin jirgin sama Stella Oduah da tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, wanda a lokuta daban-daban suka yi ta amfani da umarnin kotu wajen dakatar da shari’ar da ke yi musu.
A nasa ɓangaren, babban daraktan cibiyar kare haƙƙin al’umma da wayar da kai kan ayyukan majalisa (CISLAC), Auwal Rafsanjani, ya bayyana makamancin wannan ra’ayi.
Ya ce, wannan umarni na kotu ya saɓa wa ikon kotun ƙoli wacce ta bai wa hukumar yaƙi da cin hanci ikon binciken jami’an gwamnati. Ya bayyana cewa matakin kotun “ganganci ne irin na shari’a” wanda zai karya lagon doka da oda da jawo wa kotu zagi.