
Kungiyar Katsina Security Community Initiative (KSCI) ta bukaci gwamnati ta sauya dabarun yaki da ta’addanci a jihar.
A taron da aka yi a Abuja, shugabannin al’umma, jami’an tsaro, malaman jami’a da shugabannin gargajiya sun bayyana cewa tsofaffin dabarun da ake amfani da su ba su kawo karshen kashe-kashen da ake fama da su a yankin ba.
Shugaban kungiyar Dr. Bashir Kurfi, ya ce dole a hada dabarun soja da na tattaunawa, musamman ganin cewa mafi yawan yan bindigar yan asalin Katsina ne.
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya ce tattaunawa da jagororin Fulani ta kawo sauki a yankinsa, amma rashin daidaito a sauran kananan hukumomi na kawo cikas.
Shima shugaban karamar hukumar Kurfi, Babangida Abdullahi, ya yi korafin cewa wasu yan jihar na taimakawa yan bindiga da abinci, mai da bayanan sirri.
Shi kuwa Prof. Usman Bugaje ya zargi shiru da rashin magana da al’umma ke ci gaba da yi, a matsayin dalilin da ya sa gwamnati ba ta dauki mataki ba, inda ya gargadi cewa idan ba a dauki mataki ba, barazanar za ta bazu zuwa manyan birane.
Wasu mahalarta taron sun bukaci a karfafa kungiyoyin sintiri na vigilante domin sun fi sanin yanayin kasa da dabi’un masu laifin yankunansu.
A gefe guda kuma, rundunar soji ta sanar da kafa sabuwar bataliya a karamar hukumar Malumfashi domin kara karfi wajen yakar ta’addanci, bayan tattaunawa da yan majalisar Katsina da shugabannin rundunar soji a Abuja.