Kungiyar Izala kasa reshen jihar Kano ta shirya wani taron bita ga malaman da zasu gudanar da tafsirin Azumin watan Ramadana a kananan hukumomin 44 na jihar Kano.
Taron ya gudana ne a masallacin juma’a na Abubakar Gumi dake Mariri ‘yan goro a karamar hukumar Kumbotso.
Daya daga cikin yan majalisar zartaswa na kungiyar, Malam Ali Aliyu Abubakar ya ce, kungiyar ta shiryawa malaman bitar ne domin nusar dasu abubuwan da ya kamata su kauce musu dan samun zaman lafiya cikin al’umma.
Ya kara da cewa an horas da malaman kan dabarun da zasu yi amfani dasu wajen gudanar da Tafsiri da sauran karatu a cikin watan azumin Ramadan.
Wasu daga cikin malaman dake gudanar da tafsiri a lokacin watan Azumin Ramadan da suka halarci taron sun nuna farin cikin su bisa shirya wannan bita, tare da yin alkawarin cewa zasu yi amfani da duk abubuwan da suka koya a wajen taron.
