Ƙungiyar injiniyoyi na ƙasa ta koka kan wasu nade-nade da shugaban kasa Bola Tinubu a hukumomin kula da kogunan kasar nan.
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban kungiyar na ƙasa Margaret Oguntala.
Sanarwa ta ce kungiyar ta nuna damuwarta kan naɗin waɗanda ba su cancanta ba a matsayin waɗanda zasu jagoranci hukumomin, ciki har da hukumar ta kula da kogunan Hadejia Jama’are.
Haka zalika sanarwar ta bayyana cewa da yawa daga cikin waɗanda aka naɗa a manyan mukamai basu da kwarewar da ake buƙata don gudanar da wannan ayyukan.
Hakan ya kawo karshen zargin da ake yi wa mataimakin shugaban majalisar dattawa sanata Barau Jibrin na dakatar da naɗa ƴan jihar kano muƙamai a hukumar kula da koguna Hadejia Jama’are.