
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan babban limamin masallacin Juma’a na Maru, Alkali Salihu Suleiman da ‘ya’yansa uku da aka yi garkuwa da su a watan Maris.
Lamarin ya afku ne bayan ‘yan bindigar sun karbi miliyan 11 daga cikin miliyan 20 na kudin fansa da suka nema.
A cewar wata sanarwa da kungiyar Amnesty International ta fitar, babban Limamin mai shekaru 79 da ‘ya’yansa sun fuskanci munanan yanayi a lokacin da ake tsare da su.
“Kungiyar ta bayyana rashin jin dadinta kan yadda hukumomi suka kasa shiga tsakani da kuma kare rayukan wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
“Kuma ya kamata gwamnati ta gudanar da bincike akan kashe-kashen da ke kara yawaita domin kawo karshen sa.” In ji Isah Sunusi shugaban kungiyar a Najeriya.
Sanarwar ta kuma yi kira ga gwamnatin shugaba Tinubu da ta ba da fifiko wajen kare rayuka da kuma daukar kwararan matakai domin kawo karshen tashe tashen hankula a kasar nan.