
An zabi gwamnan ne a wannan matsayi tare da karrama shi a kasar Moroko a wani babban taro
An zabi Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif a matsayin gwarzon gwamna a nahiyar Afirka na shekarar 2025.
An gudanar da zaben ne a taron mujallar shugabanci a Afirka karo na 14 a birnin Casablanca na Kasar Morocco
Wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi daddare ta ce, an karrama gwamnan ne a matsayin wanda ya fi kowane hidimtawa ilmi, sakamakon ware kaso 31 na kasafin kudi jihar ga ilmi.
Da kuma ayyana dokar ta baci a fannin da cigaba da tura dalibai kasashe waje don karo karatu da inganta harkar lafiya da tattalin arziki da hakan ta sa Kano ta zama abar misali na kyakkyawan shugabanci a Afirka.
Tsohon Shugaban Ma’aikata Alhaji Usman Bala ne ya wakilci gwamnan a wajen taron karramawar a inda ya samu rakiyar Aisha Lawan Saji, kwamishinar al’adu da yawon shakatawa da Nazir Halliru, Babban Daraktan Hukumar Zuba Jari ta Kano da Kabir Sani Yakubu, Babban Daraktan Kamfanin Noma na Kano, da kuma Sunusi Bature DawakinTofa Kakakin Gwamnan.
baya ga gwamnan sauran wadanda akaka karrama sun hada da shugabannin kasashen Madagascar, Uganda da Tanzania da dai sauransu