
Koton Koli ta tabbatarwa da sarkin Gwandu Ilyasu Bashir sarautar Gwandu bayan shekaru 19 ana rikici kan sarautar tsakaninsa da Mustapha Jakolo.
A ranar Laraba ne Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe inda ta tabbatar da sarkin bayan da kotunan baya suka yanke hukuncin mikawa Jakolo sarautar.
A jawabinsa na yanke hukunci Mai Shari’a Emmanuel Agim ya ce, babbar kotun jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron ƙarar da Al-Mustapha Haruna Jokolo ya shigar, saboda bai bi hanyoyin sasanta rikici da dokar masarautun jihar Kebbi ta tanada ba.
Kotun ta bayyana cewa a ƙarƙashin Sashe na 5(4) na dokar, duk wanda ke da ƙorafi ya kamata ya fara miƙa ƙararsa ga Gwamnan Jihar Kebbi kafin ya kai maganar gaban kotu.
Wannan hukunci ya kawo karshen dambarwar masaurautar jihar da aka soma tun 2005