Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta bayar da umarnin a kama Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu kan aikata laifukan yaƙi a Zirin Gaza.
Sauran waɗanda Kotun ta Duniya ICC ke nema su ne tsohon ministan tsaron Isra’ila da kuma jami’an kungiyar Falasɗinawa ta Hamas.
Laifukan Kotunta bayar da umarnin kamo su a kai sun hada da zargin kisan kiyashi a yankin Falasɗinu da kuma harin da kungiyar Hamas ta kai kan Isra’ila a ranar 7 ga Oktoban 2023.
Wanda a sakamakonsa ne Isra’ila ta far wa Zirin Gaza da hare-hare ta babu kakkauta wa.
Ƙasashe da kungiyoyi da dama ne dai suka kai Isra’ila a gaban kotun kan zargin tauye haƙƙin ɗan Adam da kuma kisan kiyashin da yi wa Falasɗinawa da ke fafutukar samun ƙasarsu mai cikakken ’yanci.
Ana ikirarin sama da Falasdinawa 40,000 ne Isra’ila ta hallaka a zirin na Gaza a cikin shekara guda, da ake has ashen yawancinsu mata ne da ƙananan yara da kuma tsofaffi.
Yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza ya ɗaiɗaita rayuwar Falasɗinawa inda ta raba mutane kimanin miliyan biyu da muhallansu.
Baya ga lalata gidaje da ba za iya lissafa hakikanin adaddinsu, hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan asibitoci da makarantu da wuraren ibada da kasuwanni da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira.