Kotun ta bayyana cewa ba ta da hurumin shiga harkar masarauta.
Mai Shari’a, Muhammad Mustapha ne ya tabbatar da haka da yake jawabi yayin sauraron karar a kan rikicin masarautar Kano, kamar yadda gwamnatin Kano ta shaidawa Premier radio.
Lauyan, Barista Tudun Bashir Yusuf Tudun Wuzirce Kotu ta ce ba ta da hurumin rusa dokar da gwamnatin Kano ta yi na samar da sabuwar dokar masarauta da ta tumbuke Sarki Aminu Ado Bayero, tare da nada Malam Muhammad Sanusi na II
Premier Radio ta kira kakakin Sarkin Kano na 15, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya shaida mana cewa suna kotu, za ku ji mu da martanin bangaren sarki Aminu Ado Bayero.
An fara rikicin masarautar Kano ne tun watan Mayun 2024, bayan majalisar dokokin jihar ta amince da nadin Malam Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.