Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta ƙi amincewa da bukatar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, kwamarad Aminu Abdussalam Gwarzo, na neman a dakatar da Majalisar Dokokin Jihar daga shirin tsige shi daga mukaminsa.
A hukuncin da Mai Shari’a S.M. Shaibu ya yanke a yau Laraba, kotun ta ce mataimakin gwamnan bai cika sharuddan doka ba da za su ba shi damar samun umarnin gaggawa.
Sai dai kotun ta umurce shi da ya tabbatar an isar da dukkan takardun karar ga wadanda ake kara, domin su samu damar mayar da martani.
Wannan na zuwa ne kusan makonni biyu bayan Majalisar Dokokin Kano ta samu umarnin kotu a ranar 11 ga Maris, wanda ya hana Gwarzo ko wakilansa daukar wani mataki da zai hana majalisar gudanar da aikinta bisa tanadin sashe na 188 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Za a iya tunawa cewa majalisar ta Kano ta fara yunkurin tsige Gwarzo ne tun ranar 5 ga Maris 2026, bayan da ‘yan majalisa 38 cikin 40 suka sanya hannu kan kudirin tsige shi.
Zarge-zargen da ake masa sun hada da rashin ɗa’a, amfani da mukami don moriyar kashin kai, cin amanar jama’a, da kuma zargin karkatar da kudade masu yawa daga asusun kananan hukumomi lokacin da yake kwamishina a ma’aikatar kananan hukumomi tsakanin 2023 zuwa 2024.
