
Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta yi watsi da karar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ya shigar ya na neman a mayar masa da wasu rukunin gidaje da hukumar EFCC ta kwace a babban birnin tarayya, Abuja.
A zaman kotun na ranar Litinin, Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie ya kori karar Emefiele ya na bayyana cewa hujjojin da tsohon gwamnan ya gabatar ba su da inganci da zai sa kotu ta amince da bukatarsa.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta nemi kotun ta kwace kadarorin daga hannun Emefiele tana mai cewa gidajen mallakin gwamnatin tarayya ne.
A binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa rukunin gidajen da ke cikin wata unguwa mai masu hannu da shuni a Abuja an mallake su ne ba ta hanyar da ta dace ba.
A martaninsa, Emefiele ya ce, bai san da cewa EFCC na bincike kan gidajen ba, yana mai cewa labarin kawai ya karanta a jarida, kuma ma bai samu damar karantawa da wuri ba.
Ya ce rashin sanar da shi kai tsaye ya tauye masa damar kare kansa.
Kotu ta yi watsi da wannan hujja, inda Mai Shari’a Onwuegbuzie ya bayyana cewa an bi ka’ida wajen gudanar da binciken, kuma babu wani kuskure da zai sanya kotu ta hana EFCC ci gaba da matakin da ta dauka.
Wannan hukunci na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da tsananta bincike kan kudaden da suka bace a zamanin mulkin Emefiele a CBN, wanda ke fuskantar tuhuma da dama dangane da cin hanci da karkatar da dukiyar kasa.
Wannan mataki zai iya kara dagula lamarin shari’ar tsohon gwamnan, wanda ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga hukumomin tsaro da na bincike.