
Wata kotu a jihar Oyo ta yanke hukuncin daurin wata shida a gidan yari ga wasu mutune uku saboda wulaƙanta takardun Naira.
Mai Shari’a Uche Agomoh ya kama Amos Remilekun Ilesanmi, Olanrewaju Samuel Ilesanmi, da Ugbeh Emmanuel Ukali da laifin yin liƙi da N391,400.
EFCC ta ce mutanen sun taɓa yin zaman gidan yari a baya kan zamba ta intanet da sojan-gona.
Bayan sun amsa laifinsu, lauyansu ya nemi a sassauta musu, amma kotu ta yanke musu hukuncin wata shida ba tare da zaɓin tara ba.
Hukumar EFCC ta kama su tun watan Yuni 2024 bayan da aka zarge su da yin liƙi a wani gidan rawa da ke Ibadan.