
Babbar Kotun Tarayya da ke Yenagoa ta yanke hukunci cewa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan na da cikakkiyar damar tsayawa takarar shugabancin ƙasa a nan a zaɓen 2027.
Alkalin kotun, Isa H. Dashen, ya bayyana cewa gyaran kundin tsarin mulki na shekarar 2018 da ya ƙara sashe na 137(3) ba zai iya aiki a baya don hana Jonathan takara ba.
Wannan sashe ya haramta wa duk wanda aka rantsar da shi fiye da sau biyu a matsayin shugaban kasa to ya kammala wa’adin sa.
Masu suka sun yi iƙirarin cewa rantsuwar Jonathan ta 2010 bayan rasuwar Umaru Musa Yar’Adua da kuma zaɓensa na 2011 sun riga sun kai shi ga iyaka.Sai dai kotun ta ce Jonathan an zaɓe shi ne sau ɗaya kawai a 2011, kuma gyaran kundin tsarin mulki na 2018 ya fara aiki ne bayan ya sauka daga mulki a 2015.
Masu sharhi dai na ganin bayan hukuncin kotun, siyasar za ta ƙara zafi, inda wasu shugabannin PDP ke kira ga Jonathan da ya fara tunanin tsayawa takara a zaɓen 2027.