
Wata kotun majistire a Kano ta yanke hukuncin daurin shekara guda ko biyan tara ga wasu matasa biyu da aka samu da laifin yada bidiyoyi masu saɓawa tarbiyya a kafafen sada zumunta.
Haka na kunshe ne a wata sanarwa da Kakakin hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar a ranar Talata.
“Kotu mai lamba 47 dake zamanta a Norman’s land a Karamar Kukumar Fagge ta samu matasan ne laifin a karar da Hukumar Tace Fina-Finai da Dab’i ta Jihar Kano ce ta shigar.
“Ana zargin Matasan Ahmad Isa da Maryam Musa (Maryam Madogara), mazauna unguwar Ladanai a Hotoro, da wallafa bidiyoyin da suka ci karo da koyarwar addini da kuma al’adun Hausawa”. In ji shi.
Lauyan gwamnati mai shigar da kara Barista Garzali Maigari Bichi, ya tuhume su da haɗa baki wajen aikata laifuka masu girma a madadin hukumar.
Matasan biyu sun amsa laifukan da ake tuhumarsu da su.
Hukumar ta ce, ta dauki lokaci ma tsawo a fina-finai ta jihar ta gudanar da bincike mai zurfi kafin cafke su.
