Gwamnatin Kano ta bukaci a samar da karin rumfuman zabe a mazabun jihar Kano domin rage cunkoson da ake fuskanta a lokacin zabe.
Shugaban kwamitin wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallakar katin zabe kuma kwamishinan yada labarai Comred Ibrahim Abdullahi Wayya ne ya bukaci hakan lokacin da kwamitin ya ziyarci shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano Amb. Abdu Zango a ofishinsa.
Comred Waiya ya ce an samu karin sabbin gundumomi da unguwanni a jihar Kano wadanda su ke bukar a shigar da su cikin jadawalin hukumar, inda ya kuma bukaci a rage alkaluman rumfuman da ake samun cunkoso zuwa sabbin rumfunan zaben da za a kirkira.
Ya shaidawa shugaban hukumar cewa kwamitin zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da jihar Kano ta rike kambunta na jihar da tafi kowace jiha yawan al’umma a kasar nan.
Ya kara da cewa a shirye kwamitin yake ya yi aiki kafada-da-kafada da hukumar domin wayar da kan al’umma tare da taimaka musu ta kowace fuska.
A nasa bangaren shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano Amb Abdu Zango ya ce akwai sama da katin zabe 360,000 da har yanzu masu su basu zo sun karba na a jihar Kano.
