
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa ƴan bindiga sun kashe mutane 15 a yayin sallar Asuba ranar Talata, a wani harin ramuwar gayya da suka kai Unguwar Mantau a karamar hukumar Malumfashi.
Kakakin ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Dr. Nasir Muazu, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Katsina.
Ya ce lamarin ya faru ne lokacin da al’ummar garin ke cikin masallaci suna yin sallar Asuba, sai waɗannan ƴan ta’adda suka fara harbe-harbe cikin masallacin.
Kwamishinan ya kara da cewa harin ramuwar gayya ne kan yadda al’ummar unguwar suka yi nasarar dakile su a kwana biyu da suka gabata.
A cewarsa, mutanen Unguwar Mantau sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna inda suka kashe da dama daga cikinsu.
Bayan wannan mummunan lamari, Muazu ya bayyana cewa jami’an tsaro sun isa yankin domin dawo da zaman lafiya.
Ya ce kwamandan bangaren sojojin sama na FOB da kuma yan sanda sun isa wajen domin kawar da wadannan yan bindiga.
Gwamnatin jihar ta yaba da jarumtar al’ummar Unguwar Mantau, tare da bayyana aniyar ta na ci gaba da yaki da ’yan bindiga da tabbatar da tsaro a dukkan al’ummomi.
Gwamnatin jihar Katsina dai ta sanar da ɗaukar matakan gaggawa na ƙara dakarun tsaro a yankin Malumfashi, bayan wannan mummunan hari da aka kai ƙauyen Unguwan Mantau, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 13 a lokacin sallar asuba.