
Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 wanda za a fara yau Litinin 22 zuwa Lahadi 28, ga Satumba 2025.
Shettima na wakiltar Shugaba Tinubu ne a taro na shugabannin kasashen waje a inda zai gabatar da jawabin Najeriya a gaban zauren, tare da shiga wasu tattaunawa da tarukan a gefe da dama.
Ministan Harkokin Ƙasashen Waje Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da marawa baya tsarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen ciki har da yunƙurin samun Kujerar Dindindin a Majalisar Tsaron MDD bisa matsayar haɗin kan Afrika.
Tuggar ya kuma ce, Shettima zai kuma bayyana sabbin manufofin Nijeriya na rage hayaƙin da ke gurbata muhalli bisa yarjejeniyar Paris.
A yayin da aka tarɓe shi, Shettima ya samu rakiyar ministoci da gwamnoni ciki har da na Kaduna, Uba Sani, wanda ya ce halartar Nijeriya taron zai ƙara jawo masu zuba hannun jari ga tattalin arzikin ƙasar, musamman a fannin ma’adanai, da noma da ilimin sana’o’in dogaro da kai.
Rahotanni sun nuna cewa Shettima zai kuma shiga taron kwamitin zaman lafiya na Tarayyar Afrika, tare da ganawa da shugaban gwamnatin Sudan da sauran manyan jami’ai, domin jaddada matsayar Nijeriya kan rikicin Gabas ta Tsakiya da kuma kasar Sudan