
Mamallakan katafariyar kasuwar zamani ta Shoprite sun musanta jita-jitar kulle ilahirin kasuwancinsu da ke sassan Najeriya, wanda ke da alaƙa da durƙushewar wasu daga cikin shagunan tallata kayakinsu.
Bayanai na nuna cewa da dama daga cikin shagunan na Shoprite na fama da ƙarancin kayakin saidawa lamarin da ke nuna yiwuwar, jita-jitar ta iya zama gaskiya.
Sai dai wata sanarwa da Shoprite ya fitar, ta ce rashin kayakin cinikayyar da ake gani a rassansa ba ya nufin suna da shirin kulle shagunansu a sassan Najeriya, hasalima za su sake bunƙasa kasuwancin nasu ne.
Shoprite wanda ke da ɗimbin masu zuba jari a ciki da wajen Najeriyar ya ce durƙushewar wani sashe na kasuwancinsu na da alaƙa da halin da tattalin arziƙin ƙasar ke ciki dama tsadar rayuwa.
A cewar Shoprite, ya sauya fasalin wasu tsare-tsaren kasuwancinsa don ya zo daidai da halin da ake ciki a Najeriyar ta fuskar tattalin arziƙi.
