Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na Karfafa hadin gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin bunkasa tattalin arzikin jihar nan.
Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya bayyana haka a Gidan Gwamnati, lokacin da ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf domin karbar bakuncin Babbar Akanta ta ƙasa, Mrs Oluwatoyin Sakirat Madein wadda ta kawo ziyarar aiki jihar nan.
Ya ce duk da cewa kason kudi daga Gwamnatin tarayya na da matukar muhimmanci, sai dai Gwamnatin jihar nan tana da yakinin cewa duk jihar da za ta iya tsayawa da kafarta fannin kudin shiga, ita ce za ta fi samun ci gaba.
Hakan ce ta sa Gwamnatin jiha ta himmatu wajen kawo sauyi a fannin tasarrufi da kudade ta hanyar rungumar amfani da fasahar sadarwa don tabbatar da cewa duk wata Naira ta Gwamnati an kashe ta ta hanyar da ta dace.
Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya yabawa Babbar Akantar ta kasa bisa ziyarar wadda ya ce ta zo a kan gaba.
Ya ci gaba da cewa ziyarar za ta karfafa dangantaka tsakanin bangarorin biyu, wanda hakan zai bude sabbin damarmaki na samar da ayyukan yi tare da bunkasa walwalar jama’ar jihar nan.
A jawabinta tun da fari, Babbar Akanta ta Tarayya, Mrs Oluwatoyin Sakirat Madein ta ce ta zo Kano a wani bangare na ziyarar aiki da ta ke kaiwa ofisoshi da ma’aikata dake karkashin ofishinta a jihohi talatin da shida dake fadin tarayyar ƙasar nan.
