Jihar Kano ta zo ta daya a bikin nuna amfanin gona na kasa na shekara 2024
An gudanar da bikin ne a jihar Nassarawa inda jihar ta baje kolin albarkatun gona wanda ya zarce na sauran jihohi da hakan ya sa ta zo ta daya a farkon makon nan.
Sannan jihar ta zo ta biyu a bangaren kiwon kifi da tun daga raino har zuwa kai shi kasuwa duk a taron
Bayanin hakan ya fito ne daga wata sanarwa da Kakakin gwamnan jihar Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, Kwamishinan Kula da Aikin Gona da Albarkatun Kasa Dakta Danjuma Mahmoud ya mika wa Gwamma Abba Kabir Yusuf Garkuwar wannan nasarar a yayin taron Majalisar Zartarwar jihar karo na 22 a Fadar gwamnatin jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yaba wa Ma’aikatar da samun wannan gagarumar nasara karkashin jagorancin Kwamishina Dakta Mahmoud.
Ya kuma yi kira ga sauran Ma’aikatu da su yi koyi da wannan kokari .