
Gwamnonin Kano da Katsina da kuma Jigawa sun kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa kasuwar wutar lantarkin jihohin uku tare da zuba hannun jari a kamfanin Future Energies Africa (FEA), babban mai zuba jari a kamfanin rarraba wutar lantarki KEDCO.
Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwa da kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na jihar Kano, Dakta Gaddafi Sani Shehu ya fitar a ranar
Sanarwar ta ce, an yarjejeniyar ne yayin taron bunƙasa wutar lantarki a birnin Marrakech a Morocco, daga 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025.
Dakta Gaddafi ya ce, jihohin uku za su yi aiki tare wajen gano hanyoyin da za su amfanar da kasuwannin wutar lantarkinsu, tare da kafa tsare-tsaren doka da hadin gwiwa domin inganta aiki.