
Aminu Abdullahi Ibrahim
Al’umar garin Ajingi da aikin titi mai tsawon kilomita Biyar ya shafa sun ce suna cikin fargaba idan damunar bana ta sauka ba a gina magudanun ruwa na titin ba.
Mazauna garin sun ce ko a bara ma sun fuskanci matsalar ambaliyar ruwa saboda tsayawar aikin titin, don haka suka nemi daukin gwamna Abba Kabir Yusuf domin a dawo da aikin kafin damina ta fadi.
Salmanu Auwalu Ajingi mai shago a bakin titin da Aminu Sa’ad na kungiyar cigaban Ajingi (KADA) da wasu magidanta sun bukaci kwamishinan aiyuka Injiniya Marwan Ahmad ya taimaka ya turo dan kwangilar da aka baiwa aikin cikin gaggawa domin cigaba da aikin ba tare da bata lokaci ba.
A nasa bangaren mai rikon shugabancin karamar hukumar ta Ajingi Ashiru Jafaru Kunkurawa ya baiwa al’ummar da aikin ya shafa hakuri bisa halin da suke ciki, ya ce shugabancin karamar hukumar yana bakin kokarinsa wajen ganin an cigaba da aikin titin.
Ashiru Jafaru Kunkurawa ya ba da tabbacin cewa bayan Sallah babba gwamnati zata cigaba da aikin titin gadan-gadan.