
Ma’aikata a Najeriya sun bayyana ƙuncin rayuwar da suke fuskanta sakamakon matsin tattalin arziki da ya ta’azzara.
Hakan na zuwa ne yayin da duniya ke gudanar da bikin Ranar Ma’aikata a yau, ɗaya ga watan Mayu.
Ranar ta ma’aikata ce da aka ware a duniya don tunawa da gudummawar ma’aikata da kuma waiwayar nasarori da kalubalen da suke fuskanta.
A bikin na wannan shekara, ma’aikata da dama a Najeriya sun koka kan yadda mafi ƙarancin albashi a yanzu ba ya wadatar da su wajen biyan buƙatun yau da kullum duba da hauhawar farashin kayayyaki da kuma tashin gwauron zabi na kayayyakin masarufi.
Rahotanni sun nuna cewa har yanzu jihohi 20 daga cikin 36 ba su fara aiwatar da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 ba, duk da cewa shugaban ƙasa ya rattaba hannu kan dokar biyan sabon albashin tun ranar 29 ga Yuli, 2024.
Ƙungiyoyin ƙwadago sun sha gudanar da zanga-zanga don nuna damuwa kan irin halin da ma’aikata ke ciki, tare da kiraye-kirayen da gwamnati ta dauki matakan rage musu wahala.
Ranar ta bana, sabanin murna da shagulgula, ta kasance rana ta tunani da korafi ga dimbin ma’aikata