
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya haramtawa malaman makarantu sanya dalibai ayyukan karfi a ciki da wajen makarantun Firamare da Sakandire a jihar nan.
Gwamnan ya yi wannan gargadi a wata ziyarar bazata da ya kai makarantar koyar da harshen Larabci ta SAS da ke birnin Kano, inda ya tarar da dalibai suna tona bututun bayan gida domin gyarawa.
Gwaman ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ya ga dalibai suna gyara wajen bayan gida ba, a don haka nan take ya dakatar da daliban tare da gargadin cewa kada a sake saka daliban makarantu aikin karfi ko wanne iri.
Ya ce daga yanzu babu wani dalibi ko daliba da zasu rika yin aikin karfi a makarantun Kano da sunan horo ko kuma aikin sa kai.
A cewarsa babban makasudin tura dalibai makaranta shine daukar darasi da tarbiya da koyon sana’a, ba aikin shara ko noma ko wani aikin karfi ba.
Ya kuma yi alkawarin gyara masallacin Juma’a na makarantar da wasu gine gine dake bukatar gyara.
Da yake maida jawabi a gaban gwamnan na Kano, shugaban makarantar ya ce daliban sukanyi irin wannan aiki ne bayan tashi daga makaranta.