Jam’iyyar hamayya ta PDP, ta bayyana dalilin da ya sa za ta fara neman kudi a hannun ‘ya’yan jam’iyyar a wani mataki na kawo ƙarshen siyasar ubangida a jam’iyyar.
A cewar jam’iyyar, matakin ba shi da nasaba da rikicin shugabanci da ta ke fuskanta da kuma ficewar da ake yi a jam’iyyar.
Mataimakiyar mai magana da yawun jam’iyyar ta PDP Farida Umar, ta shaida cewa, a yadda jam’iyyar ta ke a yanzu za su mayarwa wa jama’a ita ne.
Farida Umar, ta ce Idan ana so jam’iyya ta ci gaba ai dole ne a lalubo hanyoyin da za a ciyar da ita gaba, ba wai lallai sai an jira wasu tsiraru ko masu rike da mukamai ba, don haka shi ya sa muka dauki wannan mataki.
Mataimakiyar mai magana da yawun jam’iyyar ta PDP, ta ce batun tallafawa jam’iyya ba wai lallai sai masu mulki ba, su kansu ‘ya’yan jam’iyyar akwai rawar da za su taka wajen ciyar da ita gaba, kuma komai suka bayar komai kankantarsa don a tafiyar da jam’iyya zai taimaka.
Farida Umar, ta ce ba za su fara amfani da wannan tsari ba har sai sun ji ta bakin talakawa ‘ya’yan jam’iyyar idan sun amince sai a fara amfani da shi. Idan kuwa aka samu akasin haka to sai a nemi wata mafitar.
