Hukumomi a jihar Kano sun tabbatar da rasuwar mutum 12 sakamakon hatsarin motar Kamfanin Sufurin Kano Line mallakin gwamnatin jihar.
Hatsarin ya auku ne a ranar Asabar a garin Wudil kan hanyar motar zuwa Gombe.
Wata sanarwa daga ofishin kamfanin ta ce, motar na ɗauke da mutum 16, inda 12 suka mutu ne nan take a hadarin.
“Hatsarin ya auku ne lokacin da wani direban babbar mota da ake aikin gyaran titi da ita ya juya ta a tsakiyar titi, abin da ya jawo motar bas ɗin ta ci karo da motar.
Direbobin motar su biyu, Alhaji Sabo da Alhaji Dan Azumi na cikin mutanen da suka rasa rayukansu”. In ji sanarwar.
Sauran fasinjoji biyar, huɗu mata da namiji babba ɗaya, suka ji munanan raunuka.
