Tsohon Shugaban Ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar Najeriya ta koma bin tsarin jam’iyya guda ɗaya, yana mai cewa hakan barazana ce ga zaman lafiyar ƙasa da ci gaban dimokuraɗiyya.
Jonathan ya yi wannan jawabi ne yayin wani taron karrama marigayi dattijo kuma jagoran kabilar Ijaw, Chief Edwin Clark, wanda aka gudanar a Abuja ranar Laraba.
Clark ya rasu a watan Fabrairu yana da shekaru 97 a duniya.
A cewar Jonathan, ƙoƙarin wasu ‘yan siyasa na amfani da dabaru wajen rinjayar ƙasar zuwa tsarin jam’iyya guda don cimma burin mutum ɗaya na da haɗarin jefa ƙasar cikin rikici da rarrabuwar kai.
“Duk wani yunƙuri da zai karkata Najeriya zuwa jam’iyya guda saboda son zuciya na mutum ɗaya, barazana ne ga makomar ƙasarmu,” in ji Jonathan.
Ya ƙara da cewa ko da za a rungumi tsarin jam’iyya guda, dole ne a gina tsarin ne bisa shiri da tsari mai kyau tare da cikakken fahimta daga masana da shugabanni na ƙasa.
