Fitaccen mawakin Kannywood Sadi Sidi Sharifai ya ce, ya dawo masa’antar da harkar waka kamar yadda aka san shi.
Mawakin ya fadi hakan ne a hirasa da wakilinmu a yayin wata ziyara da ya kawo gidan Radion Premier a ranar Juma’a.
Sadi Sharifai ya ce, yayi hakan ne la’akari da yadda mawakan masana’antar suke waka a yanzu.
“Na dawo masa’anatar tsundum la’akari da yadda na fahimci wasu na mafanai da yadda suke amfani da basirarasu wajen wakoki da kalaman batsa tare da bata mana suna” Inji shi.
Fasihin mawakin ya kuma bukaci abokan sana’arsa da su dinga sa kalaman yabo na fiyayayen halitttta mai tsira da aminci a wakokinsu a maimakon kalaman batsa.
Sadi Sidi Saharifai ya yi fice a Kannywood a inda yake waka da muryoyi daba-daban musamman ta marigayi dan Ibro a duk finafinai