
Akalla ‘yan gudun hijira da bakin haure 68 daga Afirka sun rasa rayukansu yayin da wasu 74 ke bace bayan wani jirgin ruwa ya kife a gabar tekun Yemen, in ji Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IOM).
Shugaban IOM a Yemen, Abdusattor Esoev, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Lahadi cewa jirgin ya ƙunshi mutum 154 ‘yan asalin ƙasar Habasha (Ethiopia), kuma ya kife a gundumar Abyan da ke Yemen.
Esoev ya ce mutum 12 ne suka tsira daga hadarin, kuma an ga gawarwakin mutane 54 a yankin Khanfar, yayin da wasu 14 aka tsinta a wani wuri daban, aka kai su dakin ajiye gawa a asibiti.
A baya, hukumomin lafiya na Yemen sun ce mutum 54 ne suka mutu.
A cikin shekaru 10 da suka wuce, mutane 2,082 aka ruwaito sun ɓace a hanyar, ciki har da 693 da aka tabbatar sun nutse a ruwa.