
Jiragen biyu sun yi karo da juna ne a sararin samanniya a wani lamari na ban mamaki a cewar rahotanni
Jirgin fasinjan kamfanin American Airlines mai ɗauke da fasinjoji 60 da ma’aikata huɗu ya faɗa cikin kogin Potomac bayan ya ci karo da jirgin yaƙi mai saukar ungulu kusa da filin jirgin saman Shugaba Ronald Reagan da ke Washington.
Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da wani jirgin saman fasinja ya yi karo da wani jirgin yaki mai saukar ungulu a sama.
Lamarin ya faru ne a kusa da filin jiragen sama na tunawa da Shugaba Ronald Reagan a ranar Laraba da dara a birnin Washington DC
“Jirgin na kamfanin jiragen PSA Airlines ya ci karo ne da jirgin yaƙi mai saukar ungulu samfurin Sikorsky H-60 a lokacin da yake kan hanyar isa filin jirgin saman”, in ji hukumar FAA mai kula da sufurin jiragen sama a ƙasar.
Jirgin na fasinja na kamfanin American Airlines na ɗauke ne da fasinjoji 60 da ma’aikatan jirgi huɗu. yayin da jirgin yaƙin mai saukar ungulu na Jami’an sojin Amurka na dauke sojoji uku.
Jirgin fasinjan ya fada cikin kogin Potomac, an kuma gano gawawwaki aƙalla 18 kawo yanzu, injia gidan talabijin na CBS a hirarsa da wani jami’in ‘yan sanda.
An dakatar da dukkanin tashi ta sauƙar jirage a filin jirgin bayan hatsarin da ya auku da misalin ƙarfe 9:00 a agogon Washington.
