
Masani a harkar tsaro ya bada shawarwari ga matsalar ‘yan bindiga dake kunnowa a jihar.
Kwararren mai suna Bala Lawan Kofar Na’isa ya ce, Kano na da damar dakile ta’addancin dake kokarin shigowa ta kananan hukumominta.
Masanin ya fadi hakan ne a hirarsa da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Alhamis.
“Barazanar tsaro na kara karfi ne a yankunan da aka kasa shawo kan matsalar da wuri.
“Kano na da sauran damar baza matakan tsaro a kan iyakokinta da kuma yankin abin da ke faruwa domin inganta tsaron yankunan da ma jihar baki daya. In ji shi.
Sai dai cimma cikakkiyar nasara kan hakan sai da taimakon alumma.
“Ya kamata dukkan al’umma su tashi domin bada bayanan sirri da ya kamata ga jami’an tsaro domin ganin an magance duk wata matsalar da ke jawo tabarbarewar tsaro a yankunan jihohin arewa”. In ji shi.
A ‘yan kwanakin nan wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun shiga Karamar Hukumar Shanono da Tsanyawa kuma wasu daga cikin kananan hukumomin jihar inda suka yi garkuwa da wasu daga mutane da kuma illata wasu daidaikun mutane.