
Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) a jihar jigawa ta bayyana mutuwar wani da ta kama mai suna Salisu Muhd mai shekaru 45 kan zargin kashe jami’inta, Bashir Adamu Jibrin, a kasuwar Shuwarin da ke karamar hukumar Kiyawa, jihar Jigawa.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar a jihar, Muhammed Badarudeen, ya fitar a Dutse ta bayyana cewa marigayi jami’in ya rasu ne yayin gudanar da aikin kama wanda ake zargi.
An ce Muhammad ya bugi jami’in da dutse a kai, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Sanarwar ta ce an kama wanda ake zargi ne a ranar 7 ga Agusta, 2025, a gidansa da ke garin Shuwarin.
Sai dai, a lokacin da ake daukar sa zuwa hedikwatar NSCDC a Dutse, ratotanni sun ce mutumin yayi kokarin tserewa daga hannun jami’an tsaro ta hanyar yin tsalle daga cikin motar da take tafiya.
NSCDC ta ce ya samu mummunan rauni inda aka garzaya da shi asibitin gwamnati a Dutse, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
NSCDCYan uwansa sun nemi rahoton likita daga asibitin Sambo Hospital Limited da ke Dutse, wanda ya nuna cewa ya rasu ne bayan tsalle daga motar da ke tafiya da gudu sosai.