Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Waiqamatus Sunnah JIBWIS ta kasa, ta bada gudunmuwar hannu da kafofin roba ga mutane 291 a jihohin Arewa maso yamma.
A taron rabon hannu da kafofin a jihar Kebbi kadai mutane 117 ne suka, wanda hakan zai ba su damar yin amfani da gabobin kamar kowa.
Mai bai wa gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin addini, Injiniya Imran Ibn Usman na daya daga cikin wadanda suka halarci bikin taron rabon.
Abdullah Diggi Shugaban kwamitin marayu na kungiyar ne ya jagoranci raba gabobin, ya kuma ce ba wannan ne karon farko ba da aka fara rabon ga wadanda suka samu lalurar rashin gabobin.
Kungiyar tana yin wannan aikin agaji ne tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta mai suna Toleram Foundation.