Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya hannu kan wani kudirin doka da zai kawo ƙarshen kwana 43 na dakatar da ayyukan gwamnati a ƙasar, bayan da Majalisar Wakilai ta amince da shi.
Trump ya bayyana cewa sanya hannunsa kan dokar zai ba da damar gwamnatin ta ci gaba da aiki kamar yadda take yi a baya, tare da tabbatar da cewa duk ayyukan gwamnati za su ci gaba ba tare da tsayawa ba.
A yayin maraba da matakin, Shugaba Trump ya soki ‘yan jam’iyyar Democrats, yana mai cewa irin wannan dakatarwa ba za ta sake faruwa ba nan gaba.
Rikicin ya samo asali ne daga rashin amincewar ‘yan jam’iyyar Democrats da buɗe ayyukan gwamnati har sai shugaba Trump ya amince da karin kudaden tallafin inshorar lafiya.
Dakatar da ayyukan gwamnati ya janyo rashin biyan dubban ma’aikatan gwamnati albashi.
