
Fim din Mai Martaba wanda yake wakiltar finafinan Najeriya a gasar lambar yabo na duniya OSCAR a Amurka
Baya ga wasan kwaikwayo na dabe da kuma finafinai yana koyarwa a Jami’ar Gwamnati Tarayya ta Ilimi watau FCE ta Kano a da.
Daya daga cikin jaruman Kannywood Ibrahim Muhammad Gumel ya kammala karatun digirinsa na uku a inda ya zama Dakta a fannin koyar da Ilimin Kimiyya fannin Physics.

Hakan ya bayyana ne wata sanarwa da Jarumin ya fitar a ranar Litinin bayan samun nasarar kare mukalar da ya gabatar a Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya wanda hakan ya ba shi damar amsa lakabin Dakta daga ranar.
A hirarsa da wakilimu ya bayyana cewa, ya karanta koyar da Ilimin Kimiyya ne na Physics a digirinsa na daya da na biyu sannan a na uku ya samu shaidar kwarewa a fannin koyar da kimiyyar ta Physics
Ibrahim Gumel ya dade yana fitowa a wasannin kwaikwaiyon dabe ciki har da na tarihin sarkin da ya kafa gidan sarautar Kano, Malam Ibrahim Dabo.
A finafinan Hausa kuma ya fito a mashahurin fin din Mai Martaba wanda ya zama zakaran gwajin finafinan da Najeriya ta shigar da shi gasar duniya na OSCAR a Amurka, a baya-baya nan.
Dakta Gumel a yanzu, shine Sakataren Kungiyar Masu Shirya finafinai Ta Kasa MOPPPAN kuma daya daga cikin jigon kungiyar Mai Nagge Cultural Troupe da Premier Radio ke tallafawa