
Jam’iyyar NNPP bangaren Farfesa Agbo Major ta kori Rabiu Musa Kwankwaso da Buba Galadima da duka wadanda ke bangaren Kwankwasiyya.
Wannan ya biyo bayan kammala babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Legas a makon nan, inda inda aka zabi Farfesa. Agbo Major a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa tare da kafa sabon kwamitin gudanarwarta.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a shalkwatar jam’iyyar da ke Abuja, Agbo Major ya jaddada aniyar jam’iyyar na bin hukuncin babbar kotun Abia da ta yanke a ranar 1 ga Nuwambar 2024, wadda ta amince da kwamitin amintattu na jam’iyyar karkashin jagorancin Dr. Boniface Okechukwu har sai an warware dukkan rikicin cikin gida.
Farfesa Major ya jaddada cewa sauyin shugabancin jam’iyyar ya bi doka, yana mai watsi da ikirarin bangaren Kwankwasiyya kan halaccin shugabancinsu.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar fahimtar juna ce ta kawo Kwankwasiyya cikin jam’iyyar a 2022 kuma zamanta a NNPP ya kare saboda yarjejeniyar da ta shigo da su ta kare, kuma sun ki bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
Jam’iyyar NNPP dai ta rabu gida inda ake da mai alamar kayan marmari bisa jagorancin Dr. Boniface, sai kuma mai alamar littafi bisa jagorancin, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Mun tuntubi shugaban jam’iyyar na Kano tsagin mai littafi, Hashim Sulaiman Dungurawa sai dai bai daga kiran da mu ka yi masa.
Musa Nuhu Yankaba, shi ne sakataren jam’iyyar NNPP mai kayan marmari a nan Kano ya tabbatar da daukar matakin.
Yana mai cewa NNPP daya ce kuma duk wanda ke bukatar dawowa bangarensu suna mara ba da shi.
Babban taron jam’iyyar NNPP mai kayan marmarin dai da aka gudanar ranar Talata da ta gabata ya amince da komawa ga tsohon tambarin jam’iyyar, yana mai watsi da sabon tambarin da bangaren Kwankwaso ya gabatar.
Ya kuma zargi mabiyan Kwankwaso da yada karya da kokarin haddasa rudani a cikin jam’iyyar duk da korarsu.

Sai dai duk da wannan tsarin NNPP Kwankwasiyya, ya ce shi ne wanda hukumar zabe ta kasa INEC ta sani.