Jami’ar Jihar Kano ta Yusuf Maitama Sule ta koma sunanta na asali na Northwest University
An yi wannan canjin suna ne a zaman Majalisar Zartarwar ta jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf a ranar Juma’a.
A wata sanarwa da Kwamishiman Kula Ilimi ami Zurfi na jihar Yusuf Kofar Mata ya wallafa a shafinsa a Facebook ya ce, an mayar da sunan Jami’ar Northwest sunanta na baya, dogaro da dalilin da yasa aka kafata a shekara 2012.
“Sannan kuma don girmama wa ga marigayi dattijo uban ƙasa Dakta Yusuf Maitama Sule, an sa wa sabuwar kwalejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari da cigaba da karatu sunansa.
“Sabuwar kwalejin Yusuf Maitama Sule College of Education and Advanced Studies, Ghari, wacce aka amince da dokar gudanarwarta a zaman majalisar, babbar makaranta ce daidai da Kwalejin Ilimi ta Rabiu Musa Kwankwaso da ke Tudun Wada.” Inji shi.
Tamkar Kwalejin Audu Bako ta Dambatta da kuma Kwalejin Malam Aminu Kano mai laƙabin Legal. Dukkaninsu manyan makarantu ne don girmamawa da tunawa da manyan mutanen jihar Kano.
Tuni majalisar zartarwar ta bada umarnin tura waɗannan dokoki zuwa Majalisar Dokoki ta jihar Kano.
Gwamnatin jihar Kano ce a karakashin Abdullahi Umar Ganduje ta sauya sunan jamai’ar a don tuna wa da MAitama Sule a lokacin da ya rasu.
.