
Kwankwaso da Gwamnan Kano a taron bikin yaye daliban
Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH) da ke Wudil ta karrama tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu fitattun mutane da digirin girmama wa Dakta.
Jami’ar ta karrama sune a bikin yaye dalibai karo na biyar da ta gudanar a harabar jami’ar a ranar Asabar a inda daruruwan dalibai suka kammala karatunsu a fannoni daban-daban na kimiyya da fasaha.
An karrama Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso – Tsohon Gwamnan Jihar Kano, an kuma yaba masa da kokarinsa wajen kafa jami’o’i da bunkasa harkar ilimi tun daga tushe.
Alhaji Aliko Dangote – wanda aka sa wa jama’i ar sunansa, an ba shi lambar girmamawa ta digirin dakta na girmamawa a bisa gudummawar da ya ke bayarwa a fannin masana’antu da ci gaban ilimi a Najeriya.
Dakta Zainab Shamsuna Ahmed – Tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya, an karrama ta bisa kokarinta wajen habaka tattalin arzikin kasa da kuma taimakawa matasa wajen samun horo da tallafi a fannin ilimi.
Professor Amina Abdullahi – Babbar malamar jami’a wadda ta shafe fiye da shekaru 30 tana bada gudummawa a fannin kimiyya, musamman a bincike da horar da matasa.
Sauran da aka karramawa sune:
Alhaji Dahiru Mangal
Alhaji Mustafa Ado Mohammad
Dakta Adeniyi Raji SAN
Babban Bako na Musamman a taron shi ne Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alh Abba Kabir Yusuf, wanda ya yaba da yadda jami’ar ke ci gaba da samar da kwararru a fannin kimiyya da fasaha. Haka kuma, ya yi alkawarin ci gaba da goyon bayan jami’ar don ta samu cimma burinta na zama cibiyar nazari da fasaha a Najeriya.
Wadanda aka karrama sun nuna godiya matuka tare da alkawarin ci gaba da bada gudummawa ga harkar ilimi da cigaban matasa. Alhaji Aliko Dangote ya ce, “Ilimi shi ne makamin cigaban kowace al’umma, kuma mu a matsayinmu na ‘yan kasuwa, wajibi ne mu bayar da gudummawa wajen habaka wannan fanni.”
Bikin ya kasance mai cike da tarihi da annashuwa, yayin da daliban da aka yaye ke cike da farin ciki da burin fuskantar rayuwa bayan jami’a. Iyaye da malamai sun nuna jin dadinsu bisa nasarar da daliban suka samu, tare da fatan Allah ya ba su nasara a gaba.
