Jam’iyyar NNPP me Kwandon Kayan Marmari ta rantsar da sabbin shugabannin ta na Jihar Kano.
Tsohon Sanatan kudancin Kanon Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa ne ya zama sabon Shugaban jam’iyyar, yayin da aka zabi Musa Nuhu ‘Yan Kaba a matsayin sakataren Jam’iyyar na Jiha.
Yayin rantsar da sabbin shugabannin, Kwamitin Amintattun Jam’iyyar na kasa Sun bukaci sabon shugabancin da suyi kokarin wajen dawo da martaba da darajar Jam’iyyar a Jihar Kano tare da tafiya tare da kowa.
Sun Kuma bayyana cewa NNPP a kasa guda daya ce mai kayan Marmari ita ce ke da rijista, ita take da takardu, kuma ita Hukumar Zabe ta sani a matsayin cikakkiyar Jam’iyya.
Taron ya samu halartar daukacin shugabannin kwamitin Amintattun Jam’iyyar na Kasa da ‘yan Majalisun dake karkashin Jam’iyyar da suka hada da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila dake wakiltar Kano ta Kudu, da ‘yan majalisar tarayya Kabiru Alhassan Rurum, Aliyu Sani Madakin Gini, sai kuma Abdullahi Sani Rogo.