
Jagoran addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce Isra’ila za ta ɗanɗana kuɗarta kan hare-haren da ta kai a cikin kasar a inda ta kashe wasu manyan jami’an sojin kasar da kuma yara kanana.
Khamane’I ya fadi hakan a safiyar Juma’a bayan da Isra’ila ta kai wasu hare-hare birnin Tehran ranar Alhamis cikin talatainin dare.
Gwamnatin Saudiya ma ta yi allawadai da hare-haren na Isra’ila a cibiyoyin nukiliyar Iran, inda a cikin wata sanarwa daga ma’aikatar harakokin wajen Saudiyya ta bayyana harin a matsayin wanda ya saɓa ƴancin Iran da tsaronta da kuma saɓa dokokin kasa da kasa.
kasar Oman da ke shirin karɓar baƙuncin tattaunawar nukiliyar tsakanin Iran da Amurka ta ce, hare-haren na Isra’ila mataki ne na takalar faɗa mai hatsari, wanda ke barazana ga ƙoƙarin tattaunawa da kuma zaman lafiya a yankin.
Japan ma ta yi allawadai da harin na Isra’ila, ta kuma yi kira ga ɓangarorin biyu su kai zuciya nesa. Ta ce zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya yana da matukar muhimmanci ga Japan.
Isra’ila ta ce, jiragen yakinta 200 ne suka kaddamar da farmakin cikin dare a Iran inda ta ce sun kai hare-hare a wurare 100 ciki har hedkwatar dakarun juyin-juya hali na kasar.
Bayan harin da kai Isra’ila ta sake daura damarar kare kai daga ramuwar gayyar dake sa ran Iran za ta dauka a kanta na barnar da ta yi, a inda ta samar da matakai daban-daban cikin har da hana taron jama’a da kuma zama cikin shirin ko ta kwana.