
Isra’ila ta ce za ta bari a shigar da kayakin agaji Zirin Gaza sannun a hankali, ta hannun ƴan kasuwa na cikin gida, amma bisa sa idonta, kamar yadda wata hukumar soji da ke kula da aikin agaji ta bayyana a jiya Talata.
Wannan na zuwa ne dai a daidai lokacin da ƙungiyoyin da ke bibiya abin da ke gudana a Gaza ke cewa matsanancin yunwa na cigaba da bayyana, lamarin da ke tasiri akan waɗanda Hamas ke garkuwa da su.
Hukumar da ke kula da gudanar da ayyuka a yankunan Isra’ila da suka hada da zirin Gaza, ta ce majalisar zartaswar ƙasar ta amince da wani tsari na faɗaɗa aikin bayar da agaji, inda za a bar aaiki hannun kamfanoni masu zaman kansu.
Hukumar ta ce kayakin da aka amince da su sun hada da kayan abinci da ake matuƙar buƙata da abincin yara, sai kuma ƴaƴan itace da kayakin tsaftace jiki.
Jami’an Falaɗinu da na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce ana buƙatar manyan motoci makare da kaya kimanin 600 su sshiga zirin Gaza a kowace rana domin biyann buƙatun jinƙai da ake da su, adadin da Isra’ila ke bari su na shiga yankin gabanin wannan yaƙin.