Dakarun Isra’ila sun tabbatar da kai hare-hare a yankin Hodeida na kasar Yemen, inda mayaƙan Houthi ke iko da shi.
Kai harin na Isra’ila martani ne kan harin da ƙungiyar Houthi ta kai filin jirgin saman Ben-Gurion na Isra’ila a ranar Lahadi.
Firaiministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani kan hare-haren Houthi kan kasar sa wanda ‘yan houthin suka ce ramuwa ne kan abin da Isra’ila ke yi wa Falasɗinawa a Gaza.
Rahotanni daga kafar yada labaran Houthi sun ce harin da Amurka ta kai a Sanaa ya raunata mutum 16.
Wannan na daga cikin jerin hare-haren da Houthi ke kaiwa Isra’ila, wanda ke nuna tsanantar sabanin siyasar yammacin Gabas.
