
Majalisar Ministocin Isra’ila ta amince da shirin da Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, dangane da tsagaita wuta a Zirin Gaza da kuma sako sauran mutanen da kungiyar Hamas ta yi gaskuwa da su.
A cikin wata takaitacciyar sanarwa daga ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu, gwamnati ta tabbatar da amincewarta da tsarin yarjejeniyar, musamman bangaren da ya shafi sakin fursunonin, duk da cewa ba ta tabo sauran sassan shirin da ake ganin za su jawo cece-kuce ba.
Wani jami’in Isra’ila da ya nemi a sakaye sunansa saboda ka’idojin gwamnati, ya ce da zarar an amince da yarjejeniyar, za a fara tsagaita wuta nan take, inda sojojin Isra’ila za su ja da baya tare da kwance damarar yaki.
Sai dai har yanzu akwai tambayoyi da ba a samu amsoshinsu ba game da cikakken tsarin tsagaita wutar musamman kan ko Hamas za ta ajiye makamai, da kuma wanda zai jagoranci Zirin Gaza bayan yakin