Isra’ila ta ce za ta bari a shigar da ‘abincin da aka fi buƙata’ zuwa Gaza domin tabbatar da cewa ”ba a samu matsalar yunwa ba.
Cikin wata sanarwa daga ofishin firayiministan ƙasar, ta ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar rundunar sojin ƙasar IDF.
Isra’ila ta ce za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin agajin bai faɗa hannun mayaƙan Hamas ba, domin hana ƙungiyar yin iko da agajin.
Isra’ila ta riƙa fuskantar matsin lamba domin ta ɗage hana shigar da agajin, inda aka hana abinci da man fetur da kuma magunguna. Bayan kwana da kwanaki da ta yi na hana kai agajin abinci zuwa yankin da ta dai dai ta da yi.
Sanarwar na zuwa ne sa’o’i bayan sojojin Isra’ila sun ce sun fara kai hare-kare ta ƙasa a duka faɗin Gaza.
