sra’ila da Hamas sun fara sabon zagayen tattaunawa a birnin Alkahira ta kasar Masar domin cimma matsaya kan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Masar na taka muhimmiyar rawa ta matsayin mai shiga tsakani, ta tabbatar da zaman tattaunawar, tana mai bayyana fatan cimma matsaya na dindindin da zai kawo ƙarshen rikicin da ya hallaka dubban Falasɗinawa.
Ministan harkokin cikin gida na Isra’ila, Gideon Saar, ya bayyana cewa tawagar Isra’ila ta isa Masar domin tantance ko akwai sahihiyar damar ci gaba da yarjejeniyar tsagaita wuta.
A halin yanzu, ana ci gaba da aiwatar da matakin farko na yarjejeniyar, inda Isra’ila ta saki fursunonin Falasɗinawa 46, ciki har da yara 24.
Wannan matakin na zuwa ne bayan samun jinkiri wajen tantance gawarwakin mutane hudu da Hamas ta mika wa Isra’ila.
Za a ci gaba da tattaunawa a birnin Alkahira yayin da ƙasa.
