
Jagoran addinin muslunci na Iran, Ayatollah Ali Khameni, ya yi watsi da duk wani tayin shiga tattaunawar kai tsaye tsakanin kasarsa da Amurka.
Bayan shafe sama da kwanaki 24 ba’aji duriyarsa ba, jagoran addinin na Iran, ya sake bayyana a ranar Lahadi tare da jaddada matsayarsa ta watsi da sake shiga tattauna wa da Amurka
Khamenei, wanda ke rike da mukami mafi kololuwar daraja a Iran ya bayyana haka ne a masallacin gidansa da ke tsakiyar birnin Tehran.
A jawabin da ya gabatar, Khamenei, ya yi shaguɓe ga wadanda ke son ganin Iran ta sake shiga tataunawa kai tsaye da Amurka, yana mai cewa matsalolin da ke tsakanin su ba za a taba warware su ba.
Matakin jagoran addinin na Iran na zuwa ne yayin da jagororin ƙungiyar Tarayya Turai da suka hada da Faransa, Jamus da Ingila su ka yi barazanar sake laftawa ƙasar takun-kuman karya tattalin arziki da aka janye mata shekaru biyu da suka gabata muddin ta ƙi amincewa ta shiga tattaunawar kai tsaye da Amurka kan batun Nukiliyarta.