Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Ƙasa IPMAN ta sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, ta haramtawa kowace motar dakon mai a kasar nan ɗaukar fiye da lita dubu 45 a fadin Najeriya.
A cewar Kungiyar matakin na daga cikin shirin da ake yi domin rage yawaitar haɗurra da kuma lalacewar tituna da ake fuskanta sakamakon lodin da ya wuce kima.
Shugaban IPMAN na Yammacin Najeriya, Chief Oyewole Akanni, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar daga Ibadan, inda ya ce matakin ya samo asali ne bayan wata ganawa ta musamman da aka yi tsakanin kungiyoyin masu ruwa da tsaki.
A cewar Akanni, daga cikin sabbin matakan da za’a fara aiwatarwa akwai wajabcin saka murfi akan kowane rami na tankar mai domin hana zubar shi a yayin hatsari, Haka zalika, an hana direbobin tankokin man zirga-zirga tsakanin ƙarfe 7:00 na dare zuwa 7:00 na safe a fadin Najeriya.
Ya ƙara da cewa IPMAN na aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro da sauran hukumomin gwamnati domin inganta tsaro a fannin sufuri da kuma dakile satar man fetur da lodin fiye da kima, wanda ke kara ta’azzarar matsaloli a fadin ƙasar.
