Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar Gamayyar Jamiyyu ta kasa reshen Kano (IPAC) ta gargadi ‘yan siyasar dake shiga kafafen yada labarai suna kalamai marasa dadi ga junansu sakamakon banbancin ra’ayi na siyasa.
Shugaban Kungiyar Alhaji Isah Nuhu Isah kuma kuma shugaban Jamiyyar ZLP a nan Kano, ya ce abun takaici ne yadda ‘yan siyasa ke fitowa a mabanbantan kafafen sadarwa suna cin zarafin junan sub a tare da la’akari da darajar da Allah ya basu ba.
Alhaji Isah ya ce manufar adawa a siyasa shine sukar duk wani abu da zai kawo tasgaro ga cigaban Al’umma ba cin mutuncin juna da nufin adawar siyasa ba.
A tattaunawar sa da wakilinmu Aminu Abdullahi Ibrahim yayin wani taron manema labarai Alhaji Isah ya ce sun shirya tsaf domin fara daukar matakai kan duk wanda aka samu da irin wadannan kalamai, domin ba za su zuba ido a lalata demukuradiyya ba.
Ya ce dole ne sai ‘yan jarida sun bayar da gudunmawa wajen hana masu yin munanan kalamai a shirye-shiryen siyasa.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda shugabannin siyasa ke cin zarafin junan su da kage da sunan dumukuradiyya.
Isah Nuhu Isah, ya ce akwai hanyoyin adawa ta hanyar kaluabalantar salon mulkin mutum ko ayyukan da yayi maimakon zagi da cin mutunci.
Ya ce zasu ɗauki matakan da suka da ce ‘yan siyasa da ke irin wadannan kalamai.
A baya bayan nan dai anga yadda ‘yan siyasa ke amfani da munanan kalamai wajen kalubalantar abokan hamayyar su musamman a kafafen sada zumunta.
